Welcome, MAIJIDDA AHMAD SHUAIBU, to the NITI Exam Hall
Please identify yourself and do a translation of the two texts below.
You have a maximum of 90 MINUTES beginning from now. Good luck.

SOURCE TEXT 1 - English-Hausa
|
|
SOURCE TEXT 2: Hausa-English
Nazarin Tarihi da Rubuta shi a Qarni na 18
Manufar malaman tarihi na wannan zamani namu ita ce binciken abubuwan da xan’adam ya yi a baya na tarihinsa domin a sami fahimta ta qwarai wajen ayyukansa. An dai sani cewa kowace qabila ta duniya tana da tarihin gargajiyarta gwargwadon qoqarinta da sha’awa tata da tarihin asalinta. Amma duk da wannan, tarihi bai zama wani abin kulawa ba a wajen jama’a kafin qarni na 18 daga haihuwar Annabi Isa (A.S) kenan. Kafin wannan qarni ba a cika mai da ilimin tarihi muhimmin abu ba a cikin rassan ilimi, domin shi ba ya bayar da amsa a kan buqatun xan’adam na gaggawa a rayuwarsa ta yau da kullum.
Yunqurin farko a kan binciken tarihi da rubuta shi kafin qarni na 18 ya fara ne daga nazari a kan abubuwan da Qibxawa da Girkawa da Romawa suka rubuta na tarihin mutanen da. Kuma a daidai wannan lokaci ne aka samu wasu manazarta wajen bincikensu na tarihi da rubuta shi. Cikin irin waxannan marubuta akwai Herodotus na Girkawa wanda bincikensa na tarihi a duniyar lokacinsa ya kawo shi har Chadi da wasu wurare a Afirka ta yamma. Haka kuma akwai Thucydides na Romawa shi ma ya yi nasa yawon binciken tarihin.
To, waxannan mutane su ne suka fara fito da bincike a kan tarihi da rubuta shit un daga qarni na biyar kafin haihuwar Annabi Isa (A.S). Amma wani abin takaici shi ne bayan waxannan manazarta sun shuxe ba a sake samun wasu manazartan irin su sun gaje sub a. Wannan kuma wata alama ce wadda ta nuna gaskiyar abin da aka faxa a baya na halayen mutane wajen rashin kulawa da tarihi. Alqur’ani mai tsarki shi ne tushen yunquri na biyu wajen binciken tarihi da rubuta shi. Domin Alqur’ani shi ne ya fito da tarihin duniya wanda aka sani da wand aba a sani ba. Saboda wannan ne binciken tarihi ya zama qarfaffan ra’ayi a addinin musulunci.